Daegu (lafazi : /tegu/) birni ne, da ke a ƙasar Koriya ta Kudu. Daegu tana da yawan jama'a 2,501,673 bisa ga jimillar 2018. An gina birnin Daegu kafin karni na biyu bayan haifuwan annabi Issa. Shugaban birni Daegu Kwon Young-jin ne.